A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da bikin kaddamar da manhajar ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Aban na shekarar 1405 (1 ga Nuwamba, 2026), tare da halartar jami’an Cibiyar Noor da wakilan Gidauniyar Isra.
Manhajar ta ƙunshi fannoni daban-daban na ilimin Musulunci, ciki har da tafsirin Alƙur’ani, falsafa, hikima, fikihu, Usulul Fiƙh, Akhlaƙ, addu’o’i da sauran ilimomin addini. Daga cikin littattafan da aka samar a cikinta akwai Tafsirin Tasnim, Rahiƙu Makhtum da kuma Sharhin Hikimatul Muta'aliya.
Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Husaini Bahrami, shugaban Cibiyar Nazarin Kwamfuta ta Ilimin Musulunci, ya bayyana cewa manhajar tana da fasaloli da suka haɗa da karanta littattafai, binciken kalmomi da bayanai, gano rubuce-rubuce masu kama da juna, da kuma binciken ayoyin Alƙur’ani a cikin littattafai daban-daban.
Ya kuma bayyana cewa masu amfani da manhajar za su iya shiga cikinta ta hanyar intanet ba tare da buƙatar sauke dukkan bayanan littattafan cikin kwamfutarsu ba.
Bugu da ƙari, Hujjatul Islam Bahrami ya sanar da cewa ana shirin samar da fasahar hira mai amfani da basirar wucin-gadi (AI), wadda za ta bai wa masu bincike damar yin tambayoyi kai tsaye kan ayyukan ilimi na Ayatullah Jawadi Amuli. Sai dai ya jaddada cewa wannan fasali yana nan a matakin shiri da bunƙasa, kuma ba ya cikin fasalolin da aka ƙaddamar a yanzu.
A nasu ɓangaren, wakilan Gidauniyar Isra sun bayyana cewa wannan manhaja wani muhimmin mataki ne wajen sauƙaƙawa masu bincike da sauran masu sha’awar ilimin addini samun damar amfani da ayyukan ilimi na Ayatullah Jawadi Amuli, tare da ƙarfafa ci gaba da amfani da sabbin fasahohi wajen yaɗa ilimin Musulunci.
Ra'ayinka